25 Satumba 2021 - 14:38
Iran : Jagora Yayi Ta'aziyyar Rasuwar Ali Landi

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan Ali Landi, gwarzon matashin yankin Izeh, dake Lardin Khuzestan, kudancin kasar, wanda ya rasa ransa a kokarin ceto makobtansu daga mummunar gobara.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A cewar shafin Jagoran, dangin Ali Landi da aka yi musu rasuwa sun samu kiran waya daga ofishin Ayatollah Seyyed Ali Khamenei; kuma an isar da ta'aziyyar jagoran, kuma an tausaya wa wannan dangin da suka rasu.

Tun da farko, shugaban kasar ta Iran Ebrahim Raisi shi ma ya mika ta'aziyyar rasuwar Ali Landi, inda ya kira shi gwarzon kasa na Iran wanda tarihin rayuwarsa zai iya zama abin karfafa gwiwa ga ‘yan Iran.

Ali Landi, mai shekaru 15 wanda ya yi kokarin ceton makwabtansa biyu daga cikin gobara ya rasu ranar Juma’a bayan ya yi mummunan kuna daga gobarar.

342/